IQNA

Masallaci Mai Tsari Na Musamman A Birtaniya

23:20 - October 07, 2017
Lambar Labari: 3481977
Bangaren kasa da kasa, masallacin cambriege masallaci ne da aka gina shi da tsari na musamman wanda ya shafi kare muhalli.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa, shafin yada labarai Cambirege News ya bayar da rahoton cewa, an gina wannan masallaci ne da tsari na musamman da aka yi amfani da fasaha.

Kudin aikin masallacin ya kai fan miliyan 15, amma har yanzu ba a kammala aikin nasa ba, duk kuwa da cewa ana shiga masallacin ana gudanar da salla a gefensa.

Abdulhakim Murad shi ne babban darakta mai kula da aikin masallacin ya bayyana cewa, bisa tsarin masallaci mutane dubu daya za su iya yi salla a cikinsa a cikin sahu a lokaci guda.

Baya ga haka kuma akwai bangarori da aka ware a cikinsa baya ga ginin masallain da ake yi salla,a kawai makaranta, da kuma dakin karatu da wuraren yin alwalla gami da wurin sayar da abinci, wanda duk aka kebe su a karkashin ginin masallacin.

Ana sa ran daga zuwa shekara ta 2018 za akammala ginin baki daya tare da kaddamar da shi, ta yadda za a fara gudanr da komaia acikinsa ahukumance.

3649782


captcha