Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na bellanaija cewa, wasu musulmi sun kirkiro da wani sharia gari Lekki da jahar Lagos domin ci gaban musulmin Najeriya da ma sauran kasashe.
Bayanin y ace shirin ya shafi karfafa ayyuka na ci gaban zamani ta hanyar na'ura mai kwakwalwa, da kuam fitar da sabbin tsare-tsare ta yadda musulmi za su tafi da sauran al'ummomin ta fuskar ci gaban kimiyya ta zamani.
Haka nan kuma masana daga cikin msuulmi sun bayyana shirin da cewa babbar dam ace da ya kamata dukkanin musulmi su yi amfani da ita, musamman ma dai matasa daga cikinsu, wadanda za su iya gudanar da ayyuka na kasuwanci da habbaka tattalin arzikinsu ta wadannan hanyoyi.