IQNA

Shugaba Rauhani A Filin Girgi Na Mehrabad:

Birnin Quds Na Palastine Ne / Kudirin Trump Kan Birnin Ba Shi Da Wata Kima

15:01 - December 13, 2017
1
Lambar Labari: 3482196
Bangaren siyasa, shugaba Hassan Rauhani a lokacin da yake a kan hanyarsa ta zuwa birnin Istanbul na Turkiya domin halartar taron shugabannin kasashen musulmi kan batun kudirin Trump a kan Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yayi kakkausar suka ga matsayar da shugaban Amurka Donald Trump na sanar da Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila yana mai cewa babu abin da hakan zai haifar in ban kirkiro wani sabon rikici a yankin Gabas ta tsakiya.

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai jim kadan bayan tashinsa zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya don halartar taron shugabannin Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) da za a gudanar a yau din nan Laraba don tattauna wannan batu da shugaban Amurkan ya tayar da kuma matsayar da ya kamata kasashen musulmi su dauka kan hakan.

Shugaba Ruhani ya ce Qudus dai ta dukkanin musulmi ne sannan kuma ita ce babbar birnin kasar Palastinu, don haka matukar dai suka kiyaye hadin kan da ke tsakaninsu, wannan matakin yana iya zama wata nasara ga musulmin da kuma yankin baki daya.

Shugaban na Iran ya kara da cewa: Sakon mu dai shi ne cewa lamarin Palastinu shi ne mafi girma da muhimmancin lamurran da suka shafi musulmi da kuma duniyar musulmi, don haka ya zama wajibi a yi Allah wadai da wannan matsaya ta Trump, yana mai sake jaddada matsayar Iran ta ci gaba da goyon bayan Palastinu da kuma Palastinawa har sai sun cimma burinsu na 'yanto kasarsu daga mamayar yahudawa 'yan share guri zauna.

3672155

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Isah Bin Abdullahi
0
0
bai kamata shugabannin kasashen musulmi su bar wannan mummunar ta'asa da shugaban Amurka yake kokarin yiba,matukar sun amsa suna musulmi.
captcha