IQNA

Wasu Makaranta Matasa Biyu Daga Rasha Suna Halartar Gasar Kur'ani Ta Azhar

22:48 - March 19, 2018
Lambar Labari: 3482489
Bangaren kasa da kasa, wasu matasa biyu daga kasar Rasha suna halartar gasar kur'ani da cibiyar Azhar ta shirya a Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na vetogate.con cewa, wadannan matasa musulmi suna halartar dukkanin tarukan gasar da Azhar ta shirya a birane daban-daban na kasar Masar.

Ahmad Junaid shugaban cibiyar shirya gasar kur'ani mai tsarki a jami'ar Azhar ya bayyana a yayin ganawa da wadannan matasa cewa, abin farin ciki ne yadda lamarin kur'ani yake kara samun wurin zama a tsakanin matasa musulmi na Rasha.

Ya kara karfafa gwiwarsu wajen ci gaba da kara bayar da himma wajen lamarin kur'ani da kuma karfafa harshen larabci.

3701247

 

captcha