IQNA

Dubban Yahudawan Sahyuniya Sun Sake Kutsa Kai Cikin Masallacin Aqsa

23:37 - September 19, 2018
Lambar Labari: 3482996
Bangaren kasa da kasa, dubban yahudawan sahyuniya ne suka kutsa kai cikin masallacin quds mai alfarma a yau.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahotn cewa, a yau dubban yahudawan sahyuniya ne suka kutsa kai cikin masallacin quds mai alfarma domin gudanar da abin da suke kira idin gafara.

Yahudawan sun kutsa kai cikin harabar masallacin ne tare da rakiyar daruruwan jami’an tsaron Isra’ila da suke dauke da makamai domin ba s kariya.

A lokacin da suke shiga cikin harabar masalacin sun lakada masu gadin masallacin duka, tare da jikkata wasu daga cikinsu.

Koa  ranar Litinin da ta gabata ma wasu daruruwan yahudawa sun shiga wannan masallaci tare da eta afarmarsa.

3748371

 

 

 

 

 

 

captcha