IQNA

Sayyid Nasrullah: Kulla Alakoki Da Isra'ila Ya Kara Fito da Fuskokin Munafukai A Fili

21:42 - November 10, 2018
Lambar Labari: 3483118
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa; kulla alakoki da Isra'ila da wasu daga cikin kasashen larabawa suke ta yi a yanzu, ya kara fito da fusakun munafukai a fili

Sayyid Nasrullah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yammacin yau a wani taro da aka gudanar a birnin Beirut na kasar Lebanon, mai taken ranar Shahid.

Sayyid Nasrullah ya ce da farko dai kungiyar Hizbullah tana yin Allah wadai da kakkausar murya dangane da duk wani yunkurinn kulla aalaka da Isra'ila da kasashen larabawa ke yi, tare da kiran su da su guji daukar irin wannan mataki na ha'intar al'ummar Palastine.

Ya ci gaba da cewa, babban abin kunya shi ne, yadda irin wadannan kasashe basa jin kunya, ta yadda suke hankoron kulla alaka da Isra'ila, a daidai lokacin da kullum rana ta Allah sai Isra'ila ta kashe Bafalastine ko jikkatawa ba tare da wani hakki ba, saboda tsabar zalunci.

Haka nan kuma wani abin mamaki da irin wadannan kasashen larabawa ha'intar 'yan uwansu larabawa da ma musulmin duniya shi ne, yadda suke mara baya ga zaluncin Isra'ila a kan 'yan uwansu Falastinawa, kamar yadda kuma su da kansu ne suke kashe 'yan uwansu musulmi larabawa a Yemen, baya ga daukar nauyin ayyukan ta'addanci, hatta al'ummomin kasashensu ba su tsira ba, matukar za su nemi hakkokinsuda kuma nuna kiyayya da zalunci, babban misalin haka shi ne kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin kasarsa.

3762697

 

captcha