IQNA

Kungiyar Boko Haram Na Ci Gaba Da Kai Hare-Hare A Najeriya

22:48 - November 16, 2018
Lambar Labari: 3483131
Bangaren kasa da kasa, kimanin mutane sha shida ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a cikin jahar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anadol cewa, mayakan kungiyar ta Boko haram sun kaddamar da hare-hare a wasu yankuna da ke cikin jahar, inda daga ranar Litin zuwa yau laraba sun kashe mutane da dama inda ya zuwa yanzu an iya samu gawawwakin mutane akalla sha shida.

Rahoton ya ce mayakan sun kashe wani manomi a  cikin gonarsa a kauyen Garimari da ke tazarar kilo mita sha uku daga birnin Maiduguri, haka nan kuma an samu gawawwakin mutane sha biyar dukkaninsu 'yan kato da gora, wadanda aka kashe su a  kauyukan Kaza Wadara da suke kusa da garin Mungunu.

Haka nan kuma rahoton ya kara da cewa, akwai mutanen da dama da ba a ji duriyarsu ba, kuma ba a san makomarsu ba, tun bayan da mayakan na Boko Haram suka kaddamar da hare-hare a ranar Litinin da ta gabata.

3764462

 

 

 

captcha