IQNA

An Bude Sabbin Makarantun Kur’ani 26 A Lardin Wadil Jadid A Masar

22:03 - January 13, 2019
Lambar Labari: 3483311
Bangaren kasa da kasa, an bude sabbin makarantun kur’ani mai tsarki guda 26 a gundumar Wadil jaded da ke kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na yanar gizo na Almisrawi ya habarta cewa, Dr. Muhammad Bukhait darakta a ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ya bayyana cewa, sun bude makarantun klur’ani guda 26 a lardin wadil jaded.

Ya ce gwamnan kardin ne ya bukaci hakan domin kara karfafa ayyukan da suka shafi kur’ania  cikin lardin nasa.

Ya kara da cewa, nan ba da jimawa ba ma’ikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar tana shirin bude wasu makarantun kur’ani guda 150 a fadin kasar.

3780644

 

 

captcha