IQNA

Ayyukan Kyamar Musulmi ta Hanyar Yanar Sun karu A Kasar Sweden

23:58 - April 19, 2019
Lambar Labari: 3483561
Bangaren kasa da kaa, wani bincike ya nuna cewa, kyamar da ae nunawa muuslmi ta hanyar yanar ta karu a kasar Sweden ta karu a tsakanin 2017 – 2018.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da arahoton cewa, cibiyar da ke sanya ido kan kalaman nuna kiyayya da batunci ta yanar a kasar Sweden (online Hate Speech Monitor) ta bayar da rahotonta na shekara-shekara, wanda ya hada shekarun 2017 da 2018.

Thomas Abrag babban daraktan cibiyar ya bayyana cewa, sun mikawa jami'an 'yan sanda sakamakon binciken nasu kamar yadda suka saba, ina sakamakon ya nuna nuna ayyukan nuna kyama da cin zarafi sun ninka har sau biyu a cikin wadannan shekaru.

Ya ce kashi 50 cikin dari na kalaman nuna kyama da in jini ta yanar gizo a kasar ta Swden, ana yinsu ne akan musulmi, sai kuma kashi 20 cikin dari a kan baki 'yan ci rani, sai kuma kashi 21 cikin daria  kan bakaken fata.

 

3804924

 

captcha