IQNA

Daftarin Dokar Hukuncin Kisa Kan Masu Keta Alfarmar Kur’ani A Zamfara

23:59 - October 17, 2019
Lambar Labari: 3484164
Bangaren kasa da kasa, an gabatar da daftrain dokar hukuncin kisa a kan duk wanda yak eta alfarmar kur’ani a Zamfara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jaridar Daily Trust cewa, Bello Muhammad Matawalle gwamnan jihar Zamfara ya tabbatar da cewa, nan ba da jimawa za a mika daftarin dokar hukuncin kisa  akan masu tozarta kur’ani mai tsarki a cikin jihar.

An dauki wannan kudiri ne bayan karbar rahoton da kwamitin mutane 24 da gwamnan ya kafa ne, dangane da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da aka yi a wata makaranta a cikin jihar ta Zamfara.

Matawalle ya kara da cewa, keta alfarmar kur’ani ba abu ne da za a lamunta da shi ba a cikin jihar Zamfara, saboda duk wanda ya aikata ya kwana da sanin cewa abin da ya aikata yana tattare da hatsari kuma zai fuskanci hukunci.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin Najeriya da ke arewa maso yammacin kasar, kuma daukacin mutanen jihar musulmi ne.

 

3850341

 

 

 

captcha