IQNA

Jagora Ya Halarci Taron Karatun Kur’ani Mai Tsarki Na Shekara-Shekara

23:51 - April 25, 2020
Lambar Labari: 3484743
Tehran(IQNA) jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya halarci taron karatun kur’ani da aka saba gudanarwa a kowace shekara tare da halartar malamai da kuma makaranta.

Ayatollah Sayyid Ali Khamenei wanda ya ke mayar da jawabi na wata wasika da malamin al’kur’ani mai girma a Iran, Muhsin Kara’ati ya aike masa, ya bayyana cewa, Hakika Allah madaukakin sarki ya ba ku samun dace a wannan fage, muna kuma rokonsa akan ya kara mu ku wannan dacen.

Jagoran ya kuma kara da cewa; Na amince da muhimmancin yin aiki tukuru wajen bunkasa koyar da al’kur’ani mai girma da kuma tafsirinsa.

Hujjatul Islam Muhsim Qara’ati ya aike wa da jagoran juyin musuluncin na Iran wasika da a ciki yake karfafa wajabcin a sake zage damtse wajen bunkasa da yada karatun al’kur’ani mai girma da tafsirinsa, haka nan kuma hukunce-hukuncen fikihun da su ke cikinsa.

A kowace shekara dai jagora yana halartar taron karatun kur’ani mai tsarki a cikin watan Ramadan mai alfarma har zuwa kasrshen watan, inda makaranta daga sassa na kasar suke halarta tare da gabatar da karatun kur’ani mai tsarki.

Har kullum jagoran yana karfafa muhimmanci mayar da hankali ga lamarin kur’ani, ta fuskar karatu da harda da kuma koyar da yara tun suna kanana.

 

 

3894129

 

 

 

captcha