Tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, a halin yanzu masallacin Sahaba da ke yankin Sharm El Sheikh a kasar Masar ya zama daya daga cikin muhimman wurare masu daukar hankali na bude ido a kasar Masar.
An gina masallacin ne tun 2011, amma ba a bude shi ba sai a cikin 2017, inda ya zama masallaci na biyu mafi girma yankin da ke cikin yankin Sinai.
Haka nan kuma an gina shi ne a wurin da yake na kasuwancin n wanda jama'a ba su yankewa.