IQNA

Tilawar Kur'ani Daga Marigayi Sheikh Saeed Sudan

19:46 - March 02, 2021
Lambar Labari: 3485705
Tehran (IQNA) Sheikh Saeed Muhammad Nur wanda aka fi sani da Sheikh Saeed, na daga cikin fitattun makaranta kur'ani shekaru masu yawa da suka gabata.

Sheikh Saeed Muhammad Nur wanda dan kasar Sudan ne, yana da kyakkyawan sauti na karatun kur'ani mai tsarki, wanda ya shahara da shi.

Daga bisani ya koma Masar da zama, inda ya ci gaba da karatun kur'ani mai tsarki, ya kuma shahara  afadin kasar ta Masar, sannan gidajen radiyon kasar suna sanya karatunsa.

Wannan malamin kur'ani ya kasance yana gabatar da karatunsa ne a masallancin Khazandar da ke yankin Shibra a cikin birnin Alkahira.

A duk lokacin da yake karatu, masallacin ya kan cika da jama'a, kamar yadda tituna da ke yankin sukan cika da jama'a masu saurare.

A lokacin da ya tafi aikin hajji, sarkin Saudiya na lokacin Abdulaziz, ya bukace da ya zauna kasar, amma Sheikh Saeed Muhammad Nur bai amince ba.

Daga bisani ya koma kasar Kuwait da zama, inda ya ci gaba da gudanar da harkokinsa a can, har zuwa lokacin da Allah ya karbi rayuwarsa, har yanzu ana saka karatunsa a gidajen rediyo na kasashen Kuwait da Masar da kuma Sudan.

3956952

 

 

captcha