A rahoton da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar, daruruwan jami’an tsaron Isra’ila ne dauke da bindigogi da kuma motoci masu sulke suka killace masallacin Aqsa a lokacin da musulmi suke gudanar da sallar Isha’i da kuma sham a daren jiya.
Bayan kammala sallar, jami’an tsaron an Isra’ila sun fara harba hayaki mai sanya hawaye a kan masallatan, kamar yadda kuma suka shiga dukarsu da kulake a lokacin da suke fitowa daga cikin masallacin mai alfarma.
Jami’an tsaron gwamnatin yahudawan sun jikkata wasu daga cikin musulmi Falastinawa da suka yi salla a daren jiya a masallacin Aqsa, yayin da kuma suka kame suka yi awon gaban da su, wadanda ba a san makomarsu ba.
Ko a daren Alahamis da ta gabata ma yahudawa masu tsatsauran ra’ayi sun kai farmaki kan masallata a cikin masallacin na Quds, tare da lakada wa wasu daga cikin musulmi da suka yi salla a wurin duka.
A ranar Juma’ar da ta gabata ma sun dauki matakan hana musulmi sun yi sallar Juma’a a cikin masallacin, amma duk da haka kimanin musulmi dubu saba’in da biyar ne suka yi sallar Juma’a a cikin masallacin Quds.