IQNA

Baje Kolin Kayayyakin Da Suka Shafi Kur'ani A Uganda

23:55 - April 29, 2021
Lambar Labari: 3485860
Tehran (IQNA) baje kolin kayayyakin da suka shafi kur'ani mai tsarki a kasar Uganda

An fara gudanar da baje kolin kayayyakin da suka shafi kur'ani mai tsarki a kasar Uganda a cikin wannan wata mai alfarma.

Wannan baje kolin dai ya kunshi abubuwa daban-daban da suka shafi kur'ani mai tsarki, daga ciki kuwa har da kwafin kur'anai da aka rubuta nau'oin rubutu daban-daban.

Daga ciki akwai wadanda suke da bugunsu an larabci, akwai wadanda an tarjama su zuwa wasu harsuna, kamar turancin Ingilishi ko kuma Faransanci, da wasu yaruka na yankin.

Baya ga haka kuma akwai wasu kayan rubutun fasaha na larabci wadanda aka rubuta wasu daga cikin ayoyin kur'ani da salo mai ban sha'awa da kayatarwa.

Haka nan kuma akwai alluna da aka yi rubutun ayoyin kur'ani a kansu, su ma da salon fasahar rubutu mai kayatarwa.

 

3967803

 

 

 

captcha