IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Hare-Haren Da Aka Kai Burkina Faso

18:38 - May 06, 2021
Lambar Labari: 3485884
Tehran (IQNA) Babban sakataren majalisar dinkin duniya ya yi Allawadai da hare-haren ta’addancin da aka kaddamar a kan fararen hula a kasar Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yayin wata zantawa da manema labarai a babban zauren majalisar dinkin duniya, mai magana da yawun babban sakataren majalisar Stephane Dujarric ya bayyana cewa, Antonio Guterres yana yin Allawadi da kakkausar murya, dangane da kisan da aka yi wa fararen hula akasar Burkina Faso.

Ya ce, abin da ya faru na kisan fararen hula a gabashin kasar Burkina Faso aiki ne na rashin imani da kekashewar zuciya, wanda ya cancanci yin tir da Allawadai, kamar yadda yadda kuma yadadda goyon bayansa ga gwamnatin kasar Burkina Faso da sauran al’ummar kasar wajen tunkarar irin wdannan ayyuka na ta’addanci, tare da jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Mayakan da ke da’awar jihadi da suke da alaka da kungiyoyin Alqaeda da kuma Daesh ne suke tsallaka iyakokin kasar daga kasar Mali, inda suke kaddamar da hare-hare a kan jama’a tare da yi musu kisan kiyashi.

Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kaddamar a gabashin kasar ta Burkina Faso, tare da lalata kaddarorin jama’a.

 

3969366

 

 

 

captcha