IQNA

Tijjani Samawi: Ranar Quds Na A Matsayin Tunatarwa Ce Dangane Da Batun Falastinu Da Masallacin Quds

18:47 - May 06, 2021
1
Lambar Labari: 3485885
Tehran (IQNA) fitaccen masani dan kasar Tunisia ya bayana ranar Quds ta duniya a matsayin ranar tunatarwa dangane da halin Falastinu take ciki.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar, a bayaninsa da ya gabatar a taron Quds na duniya da ake gudanarwa wanda Iran take daukar nauyinsa ta hanyar yanar gizo, fitaccen masani dan kasar Tunisia Dr. Tijjani Samawi ya bayana ranar Quds ta duniya a matsayin ranar tunatarwa dangane da halin da ak jefa al’ummar Falastinu da kuma masallacin Quds.

Ya ci gaba da cewa, tun daga lokacin da marigayi Imam Khomaini ya ayyana ranar karshe ta watan Ramadan a matsayin ranar Quds ta duniya, wannan yana tunatar da dukkanin musulmi da mutane masu ‘yanci da ‘yan adamtaka na duniya, dangane da zaluncin da al’ummar Falastinu suke fuskanta daga yahudawa.

Sannan kuma baya ga haka wurare masu tsarki da musulmi da kirista suke girmamawa suna fuskantar tozarci da keta alfarma daga yahudawan sahyuniya.

Ya ce raya ranar Quds, yana a matsayin raya wani lamari mai matukar muhimmanci da ya shafi al’ummar musulmi a duniyarmu ta yau.

A kan ya ce, abu da ne ya rataya kan kowane musulmi ya bayar da dukkanin irin gudunmawar da zai iya bayarwa domin domin taimakon al’ummar Falastinu da kuma ‘yantar da masallacin Quds daga mamayar yahudawa.

3969551

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Aisha Imam
0
0
Hakika lamarin Quds na musulmin duniya ne
captcha