IQNA

Ba A Gudanar Da Jerin Gwanon Ranar Quds A Birnin Tehran Ba Saboda Dalilai Na Kiwon Lafiya

Tehran (IQNA) saboda dalilai na kiwon lafiya da kuma takaita zirga-zirgar jama'a ba a samu gudanar da jerin gwanon ranar Quds ta duniya a Tehran ba.

Ba a samu damar gudanar da jerin gwanon ranar Quds ta duniya a Tehran ba saboda dalilai na kiwon lafiya da kuma takaita zirga-zirgar jama'a, amma duk da haka wasu sun yi kwarya-kwaryan gangami, sannan an gudanar da taruka ta hanyar yanar gizo.