IQNA

Daruruwan Matasa Suna Gangami A Gaza Domin Nuna Goyon Baya Ga Musulmin Birnin Quds

23:54 - May 08, 2021
Lambar Labari: 3485892
Tehran (IQNA) daruruwan matasa a cikin yankin zirin Gaza suna gudanar da gangamin nuna goyon bayansu ga al’ummar birnin Quds.

Tashar Russia Today ta bayar ad rahoton cewa, daruruwan matasa a cikin yankin zirin Gaza suna gudanar da gangamin nuna goyon bayansu ga al’ummar birnin Quds bisa zaluncin da suke fuskannta dare da rana daga yahudawan Isra’ila, da kuma keta alfarmar masallacin Aqsa.

A yau Asabar yahudawan sun hana dubban musulmi isa masallacin Aqsa domin gudanar da ibadar Lailatul Qadr, inda ko a jiya Juma’a jami’an tsaron yahudawan sun auka kan masallacin a lokacin sallar Isha’i, inda suka hana daruruwan masallata fitowa daga cikin masallacin, daga ciki akwai yara da kuma tsoffi.

Rahoton ya ce jami’an tsaron yahudawan sun rufe kofofin masallacin, sannan suka yi ta antaya hayaki mai sanya hawaye a cikin masallacin, yayin da kuma a wajen harabar masallacin daruruwan matasa ne suka taru domin nuna rashin amincewarsu da hakan.

Jami’an tsaron yahudawan sun yi ta dauki ba dadi da matasan Falastinawa a kan tituna daban-daban da suke a yankin masallacin Quds, inda suka jikkata mutane fiye da 200, suka kama wasu da dama suka awon gaba da su.

Rahoton ya kara da cewa, a daren jiya jami’an tsaron yahudawan sun kai farmaki a kan asibitin She’ar da ke cikin birnin na Quds, domin kame Falastinawa da suka samu raunuka, a yayin arangamar da aka yi tsakaninsu da matasan Falastinawan a daren jiya.Shugaban Falastinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ya jaddada cewa daukar irin wadannan matakan ba za su sanya su yin watsi da hakkokinsu ba.

Shi ma shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya ya gargadi Firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da cewa yana wasa ne da wuta.

 

3970084

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masalacin aqsa ibadar Lailatul Qadr
captcha