Hukumar Agajin gaggawa ta Falastinu wato Helal Ahmar ta bayar da bayanin cewa, karin Falasdinawa 90 ne suka jikkata a harabar Masallacin Kudus da sauran wurare a birnin Kudus yayin da jami’an tsaron Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Falasdinawa.
Hukumar bayar da agajin gaggawar ta sabunta alkaluman a safiyar yau Lahadi, inda ta ce wadanda suka jikkata sun hada da mutane 23, wadanda aka kwantar a asibiti, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na reuters ya ruwaito.
Tun da farko dai an rawaito cewa kimanin Falasdinawa 205 ne suka samu rauni a ranar Juma’a bayan da sojojin Isra’ila suka farma daruruwan Falasdinawa dake ibada a harabar masallacin na Kudus, da harsasai na roba, da hayaki mai sa hawaye, da kuma gurnet mai tsananin kara.
Kasashen musulmi da dama da suka hada da Iran, Turkiyya, Masar, Kuwait, duk sun yi tir da farmakin na Isra’ila kan Falasdinawan dake ibada a harabar masallacin na Kudus.