IQNA

Dan Kasar Tanzania Ya Zo Na Daya A Gasar Kur'ani Ta Duniya A Qatar

23:47 - May 10, 2021
Lambar Labari: 3485901
Tehran (IQNA) Abdullah Dawud Muhammad dan kasar Tanzania ya zo na daya a gasar kur'ani ta duniya a birnin Doha.

Shafin jaridar Alarabi Jadid ya bayar da rahoton cewa, Abdullah Dawud Muhammad dan kasar Tanzania ya zo na daya a gasar kur'ani ta duniya a birnin Doha na kasa Qatar da aka kammala jiya.

Abdullah Dawud Muhammad ya samu kyautar kudi da suka dalar Amurka dubu 137, sai kuma Hamza Magazi Hantur daga Masar wanda ya zo na biyu ya samu dala dubu 109, sai Hamza Warrash daga Moroco a matsayi na uku ya samu dala dubu 82.

Muhammad Hashem Muhammad daga Turkiya, da kuma Umar Aqsaqus daga Morocco, su ne suka zo na hudu da na biya, su biyun kowannensu ya dala dubu 54.

Wannan shi ne karo na hudu da ake gudanar da wannan gas a kasar Qatar, wadda ta samu halartar makaranta da mahardata kur'ani fiye da dubu biyu daga kasashen duniya daban-daban.

Baya ga kyautukan da aka bayar ga wadanda suka zo na daya zuwa na biyar, an bayar ad kyautuka ga dukkanin wadanda suka halrci gasar.

 

3970384

 

captcha