IQNA

Ayatollah Sistani: Dole Ne Musulmi Su Taimaka Ma Al'ummar Falastinu

23:13 - May 13, 2021
Lambar Labari: 3485910
Tehran (IQNA) babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya yi kira zuwa ga taimakon al’ummar Falastinu marasa kariya.

A cikin bayanin da ofishin babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya fitar a jiya, shehin malamin ya yi kira ga dukkanin musulmi da ma sauran al’ummomin duniya masu lamiri, da su taimaka ma al’ummar Falastinu, wajen taka wa Isra’ila burki a kan kisan kiyashin da take yi musu.

Bayanin Ayatollah Sistani ya yi ishara da irin mawuyacin halin da gwamnatin yahudawan Isar’aila ta jefa al’ummar Falastinu a ciki tsawon shekaru fiye da saba’in, wanda kuma har yanzu Falastinawa suna cikin wannan mawuyacin hali.

A cikin bayanin nasa, Ayatollah Sistani ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da hare-haren da Isra’ila take kaddamarwa akan al’ummar Falastinu a halin yanzu, a zirin Gaza da birnin Quds da sauran yankunan Falastinawa.

Ya yi ishara da keta alfarmar wurare masu tsarki da Isra’ila take yi musamman a cikin watan Ramadan mai alfarma, da hakan ya hada da masallacin Quds alkiblar musulmi ta farko, mafi muni kan hakan kuma shi ne shekar da jinin muuslmi a cikin wanann wuri mai alfarma a cikin watan watan Ramadan.

Daga karshe Ayatollah Sistani ya yi kira ga sauran bangarori na kasa da kasa da su sauke nauyin da ya rataya a kansu dangane da halin da ake ciki a Falastinu.

 

 

 

3971332

 

 

 

 

captcha