IQNA

Sayyid Nasrallah: Makamin Hizbullah Kariya Ne Ga Kasar Lebanon Da Al'ummarta

17:03 - May 10, 2022
Lambar Labari: 3487274
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar ce ta hana Isra’ila mamaye kasar.

A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a daren jiya da ke da alaka da zabukan kasar, Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya ja kunnen wasu ‘yan siyasa na kasar Lebanon da ke hankoron aiwatar da manufofin makiya kan al’ummar kasar ta hanyar siyasa.

Ya ce tun daga lokacin da aka kafa haramtacciyar kasar Isra’ila a shekara ta 1948, al’ummar kudancin Lebanon suke fuskantar barazana har ma da kisa da kuma korarsu daga yankunansu da yahudawan Isra’ila ke yi, kuma tun daga lokacin har zuwa cikin shekara ta 1970 babu wanda ya taka musu burki, wanda hakan ne yaa ala tilas aka kafa kungiyoyin gwagwarmaya, wadanda su ne suka tilasta Isra’ila janyewa daga Lebanon.

A kan haka Sayyid Nasrullah ya ce, Hizbullah za ta ci gaba da kasancewa a cikin dukkanin fagage na kare kasar Lebanon ta fuskar tsaro, da kuma bayar da gudunmawa a cikin harkokin gwamnati da kuma gudanar da kasa ta fuskar siyasa.

Haka nan kuma ya gargadi Isra’ila dangane da duk wani yunkuri na mamaye arzikin danyen man fetur da iskar gas a cikin ruwan kasar Lebanon, inda ya ce Hizbullah a shirye take ta kare iyakokin ruwa na kasar Lebanon ba tare da wani shayi ba.

 

4055844

 

captcha