IQNA

Musulmin Kasar Zimbabwe Sun Gudanar Da Gasar Hardar Kur’ani Mai Tsarki

22:31 - September 15, 2015
Lambar Labari: 3362967
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Zimbabwe sun gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki a karkashin kulawar majalisar musulmi ta kasar.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hqmi.org cewa, wannan gasar kur’ani mai tsarki an gudanar da ita ne tare da hadin gwiwa a tsakanin cibiyar matasa musulmi da kuma majalisar musulmin kasar tare da halartar mahardata 30 daga sassa na kasar.



Bayanin ya ci gaba da cewa gasar an gudanar da ita a bangaroru ku da suka hada da hardar izihi 15 da kuma 10 gami da 5, tare da halattar alkalai shida da suka sanya ido da kuma yin alkalanci a gasar.



Haka nan kuma an bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a gasar a dukkanin bangarori a masallacin Arkadiya tare da halartar Adam Salam shugaban majlaisar musulmin kasar Zimbabwe, Sheikh Musatafa Batiya daya daga cikin mambobin majalisar, Anubi taba wakilin Al-aun ta kasar Kuwait, Muhammad Al-ramadi wakilin cibiyar hardar kur’ani ta duniya da sauran malamai na kura’ani na kasar.



A wannan taro an karanta jawabin babbar cibiyar mahardata kr’ani ta kasa da kasa, da ke yabawa matuka dangane da yadda wannan gasa ta gudana a cikin nasara.



Haka nan kuma na gabatar da jawabai da ke kara karfafa gwaiwar musulmin kasar musamman ma matasa daga cikinsu kan muhimmancin mayar da hankali ga lamarin kur’ani da kyautata tajwidi da sauransu.

3362758

Abubuwan Da Ya Shafa: zimbabwe
captcha