IQNA

Tattaunawar Mabiya Addinai A Zimbabwe

21:52 - October 03, 2016
Lambar Labari: 3480820
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman tattaunawa kan harkokin addinai atsakanin mabiya addinai a kasar Zimbabwe.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin kula da huda da jama’a na ma’aikatar kula da harkokin al’adu cewa, a cikin wannan wata ne za a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban a kasar Zimbabwe, wanda karamin ofishin akadancin jamhuriyar musulunci zai dauki nauyin gudanarwa.

Wannan taro zai samu haartar wasu daga cikin jakadun wasu kasashen ketare domin bayyana mahangarsu kan yadda ya kamata al’ummomin duniya baki daya su samu fahimtar juna da zaman lafiya.

Kamar yadda kuma masana za su duba batun yaki da ta’addanci da duniya ke fama da shi, tare da gabatar da laccoci da kuma shawawari kan yadda za a fuskanc wannan matsala a duniya baki aya.

Wasu daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a wuri za su dauki batutuwa daban-daban domin gabatar da bayani a kansu da kuma yadda ya kamata a dauki batun ta’addanci, da kuma banbancinsa da akida irin ta dan adam balatana wani addini.

Za a mayar da hankali kan batun yadda za a yaki ta’addanci tare da hadin gwiwa tsakanin kasashe, da kuma daykar atakai na daile yunkurin kasashen da suke haifar da ta’addanci ta hanyar yda akidarsa da sunan addini a tsakanin al’ummar musuli, wanda kuma kasar da ke dauka nauyin ta’addanci da sunan addinia duniya sananniya ce ga kowa, duk kuwa da cewa da wuya kasashen turai su bayar da hadin kai kan hakan, domin suna karbar man fetur daga wurinta.

3535017


captcha