IQNA

Kasuwar ababen Halal na haɓaka a kasar Mozambique

15:48 - June 15, 2022
Lambar Labari: 3487423
Tehran (IQNA) Akwai kwararan shaidu na haɓaka tallace-tallacen kayayyakin halal a Mozambique. Wannan fadada kasuwar ya hada da karuwar kamfanonin da ke neman takardar shaidar halal da kuma tabbatar da cewa ayyukansu na halal ne ga karuwar al'ummar musulmin kasar da ke kudu maso gabashin Afirka.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, ana samun karuwar tallace-tallace da cin kayayyakin halal da suka hada da kayan abinci da kayan kwalliya a kasar Mozambique kamar yadda ake yi a sauran sassan duniya. A cewar cibiyar Instituto Nacional de Estatistica (INE), kashi 20 cikin 100 na ‘yan kasar Mozambique miliyan 32.1 Musulmai ne, daga kashi 17 cikin dari a kidayar shekarar 2007.

Tun bayan kafa hukumar Halal ta Mozambique a shekara ta 2005, kimanin 'yan kasuwa 300 'yan kasar Mozambique ne suka samu takardar shaidar halal a fadin kasar, kuma aikace-aikacen neman halal ya karu sosai tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021, inda aka samu bukatu kusan cibiyoyi 100.

Shugaban Hukumar Halal ta Mozambique ya ce "Masu neman izinin sun hada da kantuna masu sauki zuwa kantuna, gidajen cin abinci da otal-otal, masana'antun abinci da kayan kwalliya."

 A cewar Alison J. Creasey, wani Ba’amurke mai bincike a jami’ar Arkansas, musulmin Mozambique na iya biyan wasu kudade na naman halal saboda akidarsu ta addinin musulunci, ko da kuwa talakawa ne. Wannan ya zama ruwan dare musamman a yankin da musulmi suka fi yawa a arewacin Mozambik saboda tsananin tsaro da kimarsa.

Yawancin kayayyakin da aka tabbatar da halal ana shigo da su ne daga kasashen da ke makwabtaka da Mozambique, musamman Afirka ta Kudu, da kuma Gabas ta Tsakiya, Asiya da Turai, kuma Hukumar Halal ta na binciken kayayyaki da shaguna don bin ka'ida.

 

https://iqna.ir/fa/news/4064167

captcha