IQNA

Wani Dan Takfiriyya Ya Kashe Mutane Uku A Cikin Masallaci A Sudan

23:41 - March 28, 2018
Lambar Labari: 3482519
Bangaren kasa da kasa, wani dan takfiriyya ya kaddamar da farmaki kan musulmi a lokacin da suke salla a cikin masallaci a yankin Kasla na kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Sudan Tribune ta bayar da rahoton cewa, a jiya wani mutum mai dauke dn ta’a akidar kafirta musulmi ya kaddamar da hari a kan musulmi a lokacin sallar isha’i, inda ya kashe masalata uku.

Rahoton ya ce mutumin ya kaddamar da harin ne da wata shareriyar wuka da ke hannunsa, inda ya samu mutanen da suke cikin salla ya yi ta daba musu, saboda yana kallonsu a matsayin kafirai ko mushrikai bisa mahangar akidarsa.

Jama’ar da ske wurin dai ba su bari wannan dan ta’addan takfiriyya ya sha ba, domin kuwa sun lakada masa dan Karen duka, inda shi ma suka halaka shi har lahira.

3702222

 

captcha