IQNA

Jacob Herzog Shahararren Bayahuden Isra'ila A Cikin Bakuncin Masarautar Saudiyya A Riyad

23:50 - November 11, 2021
Lambar Labari: 3486543
Tehran (IQNA) Jacon Herzog fitaccen malamin yahudawa ne a Isra'ila mai tsanain kin addinin musulunci wanda a halin yanzu haka yake cikin bakuncin masarautar Saudiyya.

Tashar Al-alam ta bayar da rahoton cewa, a yau Alhamis, Moran T. bayahuden Isra’ila wanda ya shahara a shafukan zumunta, ya taya Yaqub Herzog murnar nadin da aka yi masa a matsayin malamin Yahudawa a kasar Saudiyya.
 
A shafinsa na Twitter, Moran ya sanya hoton nadin Herzog a matsayin malamin yahudawan sahyoniyawan a kasar Saudiyya, wanda masarautar Saudiyya ce ta nada shi a kan wannan matsayi domin kara dankon alkar da ke tsakaninsu.
 
Hakan dai na nuni da cewa an halatta gudanar da ibadar yahudawa a kasar Saudiyya kamar Bahrain da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, musamman ganin a baya Herzog ya bayyana cewa zai gana da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman.
 
Matakin na Saudiyya zai kara yawan tsirarun yahudawa a kasar tare da karfafa su, da kuma kama hanyar kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila a bayyane, wanda hakan yana daga cikin manufofin da ake ganin cewa yarima Muhammad bin Salman na da nufin aiwatarwa.
 
https://iqna.ir/fa/news/4012468
captcha