IQNA

Gwamnatin Sana’a: UAE Ba Za Ta Samu Kariyar Da Take Roko Daga Amurka Ba

16:02 - January 27, 2022
Lambar Labari: 3486873
Tehran (IQNA) Shugaban tawagar masu shiga tsakani na gwamnatin ceto kasar Yemen ya bayyana cewa: Hadaddiyar Daular Larabawa ba za ta kasance cikin kwanciyar hankali ba, ko da ko ta roki taimako daga Amurka,

Shugaban tawagar masu shiga tsakani na gwamnatin ceto kasar Yemen ya bayyana cewa: Hadaddiyar Daular Larabawa ba za ta kasance cikin kwanciyar hankali ba, ko da ko ta roki taimako daga Amurka,  hanya daya tilo ce mafita ga UAE shi ne ta fita daga cikin masu yaki da kasar Yemen.

Shugaban tawagar gwamnatin Yemen ta ceto kasar Yemen Mohammed Abdul Salam ya ce "kananan kasashe mambobin kawancen masu adawa da Yemen, ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa, na fama da matsalolin da su da kansu ba za iya magance su sai sun nemi taimakon Amurka da kasashen turawa.

Ya kara da cewa: " UAE ba za ta iya tsayawa da kafafunta ba kawai, sai ta nemi taimako daga Amurka ko yahudawa, a kan hakan bai kamata ta haifar ma kanta matsaloli ba, domin kuwa Amurka ba za ta kare ta ba, za dai ta yi ta karbar makuden kudadenta.

Abdul Salam ya fayyace cewa: Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta bukatar rokon taimakon Amurka, abin da take bukata shi ne ta fitar da kanta daga duk wani rikici da Saudiyya ta gayyace ta  aciki, musamman yaki kan al’ummar kasar Yemen.

A makon da ya gabata ne sojojin kasar Yamen gami da dakarun sa kai na kabilun labawan kasar suka harba makamai masu linzami da jiragen sama mara matuka a kan matatar mai da ke yankin Al-Masfa da kuma filin jirgin saman Abu Dhabi, a wani gagarumin farmaki na ramuwar gayya, bayan da UAE ta kai kan yankunan San’a da kuma saadah gami da Shibwa da ke cikin Yemen.

Kasar Saudiyya wadda ke jagorantar kawancen wasu kasashen Larabawa da Amurka ke marawa baya, ta kaddamar da farmakin soji kan kasar Yaman tare da kakaba wa kasar ta Yemen takunkumai da kuma killace tat a sama da kasa da ta ruwa, tun daga ranar 26 ga Afrilu, 2015, inda ta ce tana kokarin dawo da shugaban kasar Yemen mai murabus a kan mulki, lamarin da kuma bai yiwu ba har inda yau take.

4031694

 

 

captcha