Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, a ranar Juma’a 24 ga watan Afrilu, jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun lalata masallacin Sheikh Zakariyya mai dimbin tarihi da ke yankin Al-Darj ta hanyar kai hare-hare a gabashin Gaza.
Harin bam din da aka kai a wannan yanki ya yi sanadiyyar rugujewar masallacin da gidajen da ke kewaye da shi. An aiwatar da wannan mataki ne a cikin tsarin manufofin gwamnatin sahyoniyawan na rusa wuraren tarihi a yakin Gaza.
Babban Masallacin Sheikh Zakaria na daya daga cikin tsofaffin masallatan yankin al-Darj da ke birnin Gaza.
Babu wani bayani dangane da ranar da aka kafu, amma a wannan masallaci an binne wani mai suna Sheikh "Zakariya al-Tammari" daga cikin muftin kasar Sham, wanda ya rasu a watan Safar shekara ta 749 bayan hijira, a wannan masallaci, kuma daga baya wannan masallaci sunansa Sheikh Zakariyya. Wannan fitowar ta nuna cewa an gina masallacin da aka ambata a farkon rabin karni na 8.